Apple da Samsung za su koma kotu

Na'urorin Samsung na kamanceceniya da Apple, abinda ya kawo zargin satar fasaha.
Image caption Na'urorin Samsung na kamanceceniya da Apple, abinda ya kawo zargin satar fasaha.

Kamfanonin Apple da Samsung za su koma kotu a daya daga cikin shari'o'i masu daukar ido game da batun hakkin kirkirar fasaha.

A watan Agustan 2012 ne masu taimakawa alkali yanke hukunci suka samu Samsung da laifin keta hakkin kirkirar fasahar Apple guda shida, inda su ka ci kamfanin tarar mai girma a tarihin irin wannan shari'ar.

Ana dai daukar tarar dala biliyan guda da aka ci Samsung a matsayin gagarumar nasara ga Apple.

Sai dai a watan Maris na bana, wata mai shari'a ta ce masu taimakawa alkalin sun yi kuskure wurin kiyasta tarar da Samsung zai biya.

'kuskuren kiyasi'

A cewar mai shari'a Lucy Koh dala miliyan 550 na tarar an kiyasata su daidai amma akwai kuskuren wurin kiyasin ragowar dala miliyan 450.

Hakan na nufin za'a iya rage adadin ko ma a kara a sabuwar shari'ar da za'a gudanar.

Tun asali dai kamfanin Apple ya nemi Samsung ya biya shi diyyar dala bilyan biyu da miliyan 500 ne.

Apple ya zargi Samsung da satar samfurin wayar iPhone da kwamfutar iPad, da kuma fasahar sarrafasu irinsu latsa fuskar na'ura domin kara girman hoto.

Sai dai Samsung ya ce ya fara kirkiro na sa wayoyin tun kafin Apple ya bayyana kudirin kaddamar da iPhone. Don haka ya bukaci Apple ya biya shi dala miliyan 519 saboda bata suna.

A yanzu haka dai akwai Samsung da Apple na shari'a da junansu a kotunan kasashe fiye da 10 na nahiyar Turai.

Sai dai wasu kwararru kan harkokin fasaha na ganin rikicin shari'ar na da mummunan tasiri kan masu sayen kayan kamfanonin.