ASUU ta dage taro saboda makokin Iyayi

Malaman jami'o'in Nigeria sun sha arangama da 'yan sanda a yayin zanga-zanga.
Image caption Malaman jami'o'in Nigeria sun sha arangama da 'yan sanda a yayin zanga-zanga.

Kungiyar malaman jami'o'in Nigeria ASUU ta dage taron kolin da ta shiryawa gudanarwa a Kano domin tattauna makomar yajin aikin da ta fi watanni uku ta na yi.

ASUU ta dage taron ne sanadiyyar mutuwar tsohon shugabanta Farfesa Festus Iyayi a hatsarin mota kan hanyarsa ta halartar taron.

An dai sa ran kungiyar za ta dakatar da yajin aikinta ne a taron da ya biyo bayan tattaunawar rassan kungiyar kan tayin da shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi musu.

Farfesa Iyayi, wanda ya jagoranci kungiyar daga 1986 zuwa lokacin da gwamnatin soji ta wancan zamani ta soke ta a 1988 ya rasu ne a Lokoja bayanda motarsa ta yi karo da jerin gwanon motocin gwamnan jihar Kogi, kyaftin Idris Wada.