Morsi zai shigar da soji kara a kotu

Image caption Morsi nada miliyoyin magoya baya a Masar

Hambararren Shugaban Masar, Mohammed Morsi zai shigar da sojin kasar da suka cire shi a kan mulki gaban kuliya bisa zarginsu da cin amanar kasa.

A wata wasika da lauyoyinsa suka karanto, sun ce ba za a samu zaman lafiya ba a kasar, har sai an maida shi kan mulki sannan a hukunta wadanda suka yi masa juyin mulki.

Lauyoyin sun karanto wasikar ce kwana guda bayan sun tattauna da Morsi wanda a yanzu haka yake tsare a kurkuku.

A sakon, Mr Morsi ya ce ministan tsaron kasar, Janar Abdel-Fattah el-Sissi ya ci amanar Masar baki daya.

A makon da ya gabata ne, aka kai Mr Morsi kurkuku bayan da aka gurfanar da shi gaban kuliya bisa zargin tunzura aikata kisan kai.

A baya dai an tsare shi ne a wani kebantaccen wurin soji tun bayan da aka hambarar dashi daga kan mulki.

Karin bayani