Mutane miliyan sha daya mahaukaciyar guguwa ta shafa a Philippines

Image caption Hukumar ta kara da cewar ga baki daya bala'in guguwar ya shafi mutane miliyan 6.9 ne.

Gwamnatin Philippines ta ce illar da mahaukaciyar guguwar nan ta ranar Juma'a, da aka yi wa lakabi da Haiyan wadda ta shafi mutane miliyan 11, ta yi a kasar ta tayar mata da hankali matuka.

Sakataren majalisar ministocin kasar Rene Almendras ya ce, kasar tana fuskantar kalubalen samar da kayayyaki da ba ta taba fuskanta ba, yayin da take kokarin samar da ruwa da abinci da agajin kula da lafiya ga mutanen da suka tsira daga bala'in.

Wakiliyar hukumar lafiya ta duniya a kasar ta philippines Dr Julie Hall ta ce mutane da dama da suka tsira har yanzu ba su kai ga samun taimako

Ta ce, ''akawi mutane da dama a rana ta biyar da basu da mafaka ba su da abinci ba su da ruwa''

Ana shirin fara aikin bayar da agaji na kasashen duniya, a filin jirgin saman Tacloban, birnin da guguwar ta daidaita baki daya.

Manyan motoci dauke da kayayyaki suna shiga cikin birnin , yayin da su kuma sojin ruwa na Amurka ke kokarin kaiwa ga yakunan da ke da wahalar shiga.

Karin bayani