APC ta nemi afuwar Shekarau

Shekarau da Buhari da Bola Tinubu
Image caption Bangaren Shekarau a Kano sun yi zargin jam'iyyar APC tai musu ba daidai ba

A wani yunkuri na dinke barakar da ake ganin tana neman kunno kai tsakanin shugabannin jam'iyyar hamayya a Nigeria APC na kasa da kuma wasu 'yan jam'iyyar a Kano, wani kwamitin bawa juna hakuri ya ziyarci Kano inda ya gana da 'yan jam'iyyar.

Su dai 'yan jam'iyyar karkashin Malam Ibrahim Shekarau na ganin shugabannin jam'iyyar na kasa sun musu ba dai-dai ba, a lokacin da suka kai ziyarar gayyatar gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso zuwa cikin jam'iyyar ba tare da sanin 'yan APCn a Kano ba, ba kuma tare da an yi dasu ba.

Lamarin dai, yaso ya tada jijiyar wuya tsakanin 'yan jam'iyyar, abinda ke nan yasa aka kafa kwamitin rarrashi.

A wata hira da BBC Malam Ibrahim shekarau ya ce wannan kuskure ne, kuma zasu zuba ido suga ko za a gyara irin wannan kuskure nan gaba.

Dama can wasu manazarta siyasar Najeriya sun yi hasashen za a iya samun irin wannan baraka a cikin jam'iyyar ta APC.

Karin bayani