Za'a daure jigogin siyasar Brazil a jarun

Jose Dirceu da tshohon shugaba Lula
Image caption An kama Jose Dirceu da laifin biyan 'yan adawa su goyi bayan tshohon shugaba Lula.

Kotun kolin Brazil ta ba da izinin daure 'yan siyasa da 'yan kasuwa da aka samu da laifi a shari'a mafi girma kan cin hanci da rashawa da aka gudanar a kasar.

Fiye da mutane 20 aka samu da laifin tsoma hannu a badakalar biyan 'yan adawa su goyi bayan gwamnatin tsohon shugaban kasa Luiz Inacio Lula da Silva.

Hakan na nufin nan ba da dadewa ba za'a yi daure tsohon babban jami'i a fadar shugaban kasar Jose Dirceu tare da fitattun 'yan siyasa da manyan 'yan kasuwa na kasar.