Ranar yaki da ciwon sukari

Gwajin ciwon sukari
Image caption Gwajin ciwon sukari

Yau ce ranar yaki da ciwon sukari ta duniya, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta kebe a duk shekara domin kara fadakar da jama'a game da ciwon na sukari, da kuma halin da wadanda ke fama da cutar ke ciki.

Wasu alkaluma na hukumar lafiya ta duniya dai na nuni da cewa mutane sama da miliyan dari uku da hamsin ne ke fama da cutar ta Suga a fadin duniya.

An ce da dama daga cikinsu na kasashen Afirka ne irinsu Nijeriya.

A irin wadannan kasashe masu fama da cutar na kira ga gwamnatoci da su taimaka masu wajen sayen magungunan da ke da tsada.