An sace fadan coci bafaranshe a Cameroon

Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius
Image caption Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius

Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta ce an sace wani fadan coci dan kasar a arewacin kamaru.

An sace fada Georges Vandenbeusch ne kusa da garin Koza mai nisan kilomita 30 daga iyakar Nigeria.

Yankin ya yi kaurin suna kan satar mutane domin garkuwa da su, inda a bana mayaka masu kishin Islama suka sace wani iyalin Faransawa su bakwai, suka rike su tsawon watanni biyu.

Faransa ta ce ta gargadi mutane cewa yankin na da hadari, amma fadan cocin ya zabi ya zauna a yankin domin cigaba da aikinsa.