Mahara sun kashe 'yan Ashura 20 a Iraq

Ashura
Image caption 'Yan Shi'a na tunawa da kisan Imam Hussein lokacin Ashura

Masu harin bama-bamai kan 'yan Shi'a a Iraq sun kashe fiye da mutane 20 tare da raunana wasu da dama.

Hare-haren dai na zuwa ne daidai Ashura, lokacinda yafi kowanne muhimmanci a wurin 'yan Shi'a.

Wani dan kunar bakin wake ya hallaka akalla mutane 15 da ke jerin gwano a birnin Al Sadiya a lardin Diyala.

Jami'ai a garin Hafriyah, da ke kudu da Baghdad sun ce akalla mutane takwas ne suka rasu lokacin da bama-bamai biyu suka tashi a tare.

'Yan Shi'a na amfani da lokacin Ashura domin tuna kisan jikan manzon Alllah sallal lahu alaihi wasallam, Imam Hussein.