Majalisa ta gayyaci hafsoshin tsaron Nigeria

Jami'an tsaron Najeriya
Image caption Gwamnatin Najeriya na neman tsawaita dokar- ta- baci a jahohin Borno da Yobe da Adamawa

A Najeriya, a yau ne ake sa ran manyan hafsoshin tsaro na kasar zasu bayyana gaban Majalisar wakilan kasar.

Manyan Hafsoshin Najeriyar zasu yiwa 'yan Majalisar bayani ne game da yanayin tsaro a jihohin Borno da Yobe da kuma jihar Adamawa, sakamakon dokar ta- baci da aka sanya a jihohin.

Majalisar dai ta dauki wannan mataki gabannin muhawara da zata yi dangane da bukatar da shugaban kasar ya gabatarwa 'yan Majalisun, na neman kara wa'adin dokar ta-baci a jihohin, wanda ke karewa a yau.

'Yan majalisun dai na bukatar Manyan Hafoshin sojin su fada musu irin nasarorin da aka samu a wadannan jahohin uku da aka sanyawa dokar- ta- baci.

Tuni dai majalisar dattawan kasar ta amince da wannan bukata ta Shugaban Kasa.

Kara wa'adin dokar- ta- bacin a wadannan jihohi uku dai ya janyo cece-kuce a cikin kasar.

Karin bayani