''Yancin zirga-zirga a Afirka na janyo cikas'

Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria da Muhammadou Issoufou na Niger
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria da Muhammadou Issoufou na Niger.

Hukumar hadin-gwiwa don bunkasa Najeriya da Niger ta bayyana cewa dokar da ta bada 'yancin zirga-zirga a tsakanin kasashen dake shiyyar Afirka ta yamma na daga cikin abubuwan dake janyo tarnaki a yakin da kasashen biyu ke yi da ta'addanci.

Hukumar ta ce wasu miyagu kan rabe da wannan dokar su shiga kasashen juna, da nufin yin aika-aika.

Baya ga bunkasa harkokin tattalin arziki, inganta tsaro na daga cikin ayyukan da gwamnatocin Najeriya da Nijar suka dora wa wannan hukuma ta hadin gwiwa, musamman a baya-bayan nan da Kasashen ke fuskantar kalubale ta fannin tsaro da suka ce ba su taba ganin irinsa ba a tarihin wanzuwarsu.

Sai dai hukumar ta ce an samu ci gaba sosai wajen yaki da hare hare da kuma rage yaduwar makamai tsakanin kasashen biyu sakamakon matakan da hukumar ke dauka na inganta sintiri akan iyakokin kasashen.

Karin bayani