An sace shanu sama da 1000 a Pilato

Satar shanu kan haddasa rikici a Nigeria
Image caption Satar shanu kan haddasa rikici a Nigeria.

Makiyaya a jihar Pilato da ke tsakiyar Nigeria sun ce an sace musu shanu fiye da dubu guda a jiya.

Sakataren kudi na kungiyar Miyatti Allah ta Fulani makiyaya reshen jihar Pilato Malam Salihu Jauro ya ce lamarin ya faru ne a kauyen Sit dake tsakanin Pankshin da Langtan ta arewa.

Makiyayan na neman mahukunta da su basu cikakken tsaro tare da dabbobinsu.

A mafi yawan lokuta dai satar shanu na haddasa rikicin kabilanci a yankin.

Jihar Pilato ta sha fama da rikicin kabilanci da addini tsawon shekaru 14.