An zargi 'yan sandan Najeriya da wuce iyakokinsu

Shugaban 'yan sandan Najeriya MD Abubakar
Image caption 'Ana amfani da 'yan sanda wajen hana gudanar da Taruka'

A Najeriya, Kungiyoyin da ke rajin kare demokuradiyya sun fara kokawa game da yadda rundunar 'yan sandan kasar ke hana gudanar da Taruka .

Cibiyar raya demokuradiyya ta Centre for Democracy and Development dake Abuja, ta yi zargin cewa masu iko na amfani da jami'an 'yan sanda wajen takurawa abokan hamayyarsu.

Haka a cewar cibiyar kuma zai iya zubar da kimar 'yan sandan tare da kassara mulkin demokuradiyya a Najeriyar.

Cibiyar dai ta bada misalai ne da yunkurin da 'yan sandan sukayi a baya bayan nan na hana wasu tarukan siyasa a Kasar.

A kwanakin baya ne dai majalisar dokokin Najeriya ta bukaci Shugaban 'yansandan Najeriyar Alhaji MD Abubukar da ya zo ya yi bayani game da dalilin da yasa 'yan sanda suka yi yunkurin hana wani taron Gwamnonin PDP sabuwa.

An jima dai ana zargin 'yan sandan Najeriya da wuce gona da iri wajen gudanar da aikinsu, zargin da rundunar 'yan sandan ta sha musantawa.

Karin bayani