'Mata masu karancin shekaru na mutuwa wajen haihuwa'

Mace mai juna biyu
Image caption Matsalar ta fi kamari a Kasashen Afirka

Rahoton Majalisar dinkin duniya na wannan shekara dangane da batun yawan al'umma, ya nuna cewar haihuwar da 'yammata suke yi wadanda basu kosa ba, ita ce ke sanadin yawaitar mutuwar su musamman a lokacin da suka je haihuwar.

Majalisar dinkin duniyar tayi gargadi kan cewar yawan haihuwar yara mata masu karancin shekaru na ci gaba da karuwa a duniya.

A cewar rahoton, matsalar tafi kamari a kasashen dake shiyyar Afrika ta yamma.

A Ivory cost cikin adadin 'yammata 10 daya cikinsu ta taba fuskantar haihuwa tana da karancin shekaru.

To amma a Kasashen Guinea da Mali dake makwabtaka da Ivory cost, rahotan na majalisar dinkin duniya yace rabin 'yan matan dake haihuwar masu karancin shekarun 'yan shekaru 20 zuwa 24 ne.