Yau ake zaben Gwamna a Anambra

Zaben Najeriya
Image caption Al'ummar jahar Anambra za su zabi Gwamnan su

A Najeriya, yau jama'ar jihar Anambra kusan miliyan biyu zasu je rumfunan zabe 4,600, su kada kuri'a a zaben gwamnan jihar da aka shirya gudanarwa.

'Yan takara ashirin da uku ne zasu fafata a karkashin inuwar jam'iyyu daban-daban.

Hukumar zabe da hukumomin tsaro sun ce sun yi shirye-shiryen da suka kamata don ganin an gudanar da zaben cikin nasara, kuma lami lafiya.

Hukumar zaben Najeriya ta bayyana cewa kawo yanzu ta tura jami'an zabe 12,622 zuwa kananan hukumomi 21 da kuma nasu sa'ido 120.

Za a gudanar da zaben karkashin yanayi na tsaro.

Karin bayani