An yanke wa dan Boko Haram daurin rai-da-rai

Image caption Mustapha zai kasance a jarun har karshen rayuwarsa

Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja, baban birnin Nigeria ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga mutumin da ake zargi da dana bom a wadansu gidajen jaridun kasar.

Kotun, wacce mai shari'a Adeniyi Ademola, ke jagoranta ta samu Umaru Umaru Mustapha, mai shekaru 34 a duniya da laifin aikata ta'addanci a watan Afrilun shekarar 2012, lokacin da ya tashi bom a ofishin jaridun ThisDay da Moment da kuma The Sun da ke Kaduna.

Mai shari'a Ademola ya ce, "Na kama ka da laifin da ake zarginka da aikatawa, don haka na yanke maka hukuncin daurin rai-da-rai tare da aiki mai tsanani''.

An dai kama Mustapha ne a motarsa bayan ya jefa bama-bamai a ofisoshin jaridun, kuma ya yi yunkurin tserewa.

Karin bayani