Kauyawa sun kurewa damisa gudu a Kenya

Image caption Kauyawan sun kurewa damisar gudu

Wasu mutanen kauye a arewa maso gabashin Kenya sun kurewa wasu damusa biyu da ke cinye musu akuyoyi gudu, sannan suka kama su.

Mai awakin ya shaidawa BBC cewa damusar suna yi wa dabbobinsa dauki dai-dai kusan kulli yaumin.

Mutanen da suka kama damisar sun jira ne sai da rana ta kwalle, sannan suka bi su da gudu har fiye da tsawon kilimita shida kafin su kama su.

Ina so a bani diyya

Damisar dai sun gaji da gudu shi ya sa ma suka sare, lamarin da ya bai wa kauyawan damar kama su.

Sun kama su ne a raye, kana suka mika su ga hukumar kula da gandun daji ta Kenya.

Mai akuyoyin, Nur Osman Hassan, ya shaidawa Sashen Somalia na BBC cewa,"Ina so a biya ni diyya saboda damisar sun cinye mini akuyoyi da dama''.

Masu aiko da rahotanni sun ce dabbobi ne kashin-bayan tattalin arzikin 'yan kasar Somalia da ke zaune a arewa maso gabashin Kenya.

Karin bayani