Gwamnonin Najeriya za su gana a Sakkwato

Wasu Gwamnonin Najeriya
Image caption Alamu sun nuna cewa Gwamnonin dake goyawa Rotimi Amaechi baya ne kadai za su halarci Taron.

Kungiyar Gwamnonin jahohin Najeriya karkashin Gwamnan jahar Rivers Rotimi Ameachi na jahar Rivers za ta gudanar wani taro domin tattauna matsalolin kasar a birnin Sakkwato dake arewacin Najeriyar.

An samu rabuwar kai a kungiyar Gwamnonin Najeriyar ne tun bayan zaben da aka yi na wanda zai Shugabanci Kungiyar Gwamnonin, inda Gwamnan Jahar Filato da na Patakwal kowannensu ke ikirarin cewa shine halartaccen Shugaba.

Akwai dai alamun dake nuna cewa Gwamnoni 19 ne kadai za su halarci taron.

A wajen wannan taron ne kuma ake sa ran Gwamnoni bakwai na sabuwar PDP za su cimma matsaya kan ko su sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta APC ko kuma a'a.

Gwamnonin sabuwar PDPn bakwai sun hada da Gwamnan jahar Kano da na Sakkwato da na Jigawa da Niger da Adamawa da kuma na Kwara da na Patakwal.

Babbar jam'iyyar adawa ta APC a Najeriya dai ta jima ta na zawarcin wadannan Gwamnoni.

Wannan dai shi ne karon farko da Gwamnonin ke taro a wajen babban birnin kasar, Abuja.

Karin bayani