Philippines: mutane 3,500 ne suka rasu

An samu agaji a Philippines amma karancin motoci ya hana shi isa ga mabukata.
Image caption An samu agaji a Philippines amma karancin motoci ya hana shi isa ga mabukata.

Gwamnatin Philippines ta ce kawo yanzu an tabbatar da rasuwar mutane 3,500 sanadiyyar mahaukaciyar guguwar Haiyan, a yayin da ake cigaba da fadi-in-fada game da adadin wadanda suka rasu.

Kiyasin majalisar dinkin duniya ya ce adadin ya zarta haka sosai kuma akwai yiwuwar gano karin gawarwaki bayanda masu kai agaji suka fara kutsawa yankunan karkara.

Yanzu dai agaji daga kasashen waje na ta kwarara zuwa Philippines sai dai gwamnatin ta ce tallafi baya isa ga mabukata saboda karancin motocin diban kaya.

Jirage daga jirgin ruwan Amurka mai daukar jiragen sama sun fara kai agaji zuwa garin Guiuan da ke gabar tekun Pacific inda mahaukaciyar guguwar ta fara sauka.