An tsare 'yan ci-rani 50,000 a Saudiyya

Image caption 'Yan ci rani a Saudiyya

An tsare 'yan ci-rani kimanin 50,000 a Saudiyya, a kokarin da mahukuntan kasar ke yi na korar ma'aikata 'yan kasashen wajen da basu da cikakkun takardu.

Hukumomin Saudiyyar sun yi amfani da motocin bas-bas wajen kwasar 'yan Ethiopia su fiye da dubu 20, zuwa wata cibiya da ke wajen birnin Riyadh, inda za a tsare su na dan lokaci, kafin a tasa keyarsu zuwa gida Ethiopia.

Mahukuntan sun dauki matakin ne, bayan zanga-zangar da ma'aikata 'yan Ethiopia suka yi a wata unguwar Riyadh, inda akalla mutum daya ya rasa ransa a artabun da ya biyo baya.

'Yan Ethiopiar sun yi kira ga jama'a a kafofin sada zumunta na internet, da su fito su yi tarurukan gangami a gaban ofisoshin jakadancin Saudiyya, a ko'ina a duniya, domin yin Allah wadai da matakin da Saudi Arabiyar ke dauka a kan 'yan kasarsu.

Karin bayani