Brazil:Hukunci kan cin hanci da rashawa

Alkali a kasar Brazil
Image caption Alkali a kasar Brazil

Kasar Brazil ta yanke hukuncin dauri kan manyan 'yan siyasa, 'yan kasuwa da ma'aikatan bankuna kan aikata laifin cin hanci da rashawa.

Wannan ita ce shari'ar aikata cin hanci da rashawa mafi girma da aka taba samu a kasar da aka fi sani da ''Mensalao'' ko kuma ba albashin wata mafi girma.

Cikin manyan kusoshin da suka mika kansu ga jami'an 'yansanda sun hada da hafsan hafsoshin tsohon shugaban kasar Luiz Inacio Lula da Silva, Jose Dirceu da kuma tsohon shugaban jam'iyar ma'aikata da har yanzu ke mulkar kasar Jose Genoino.

Wannan wani lokaci ne da 'yan kasar Brazil da dama ke tunanin ba zasu taba gani ba a kasar ba, da matsalar cin hanci da rashawa ta yi katutu a tsakanin 'yan siyasa da 'yan kasuwa.

Jam'iya mai mulki dai ta yi watsi da yanke hukuncin da cewa anyi amfani da siyasa ne.

Amma kuma masu sa ido da dama cewa suke wannan wani muhimmin mataki ne ga kasar ta Brazil, yayinda take kokarin mayar da kanta jimkakkiyar kasa a fannonin tattalin arziki da siyasa.