Zaben gwamna a jihar Anambra

masu zabe a Najeriya
Image caption An dauki matakan tsaro sosai domin gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali

Rahotanni daga jihar Anambra a Nijeriya na cewa akwai karashen zabe da za a yi a ranar Lahadi a wata mazaba ta bakwai dake Obosi kusa da birnin kasuwancin nan na Onitcha.

'Yan takara ashirin da uku ne suka fafatawa a zaben.

Kuma rahotanni na cewa an samu fitar jama'a sosai a wasu yankunan.

Wakilin BBC a Anambra ya ce an soma tattara sakamakon zaben tun daga ranar Asabar.

Ya ce ana kuma kyautata samun sakamakon zaben a ranar lahadi.