Cameron ya sake tayar da kura a Sri Lanka

Praministan Birtabiya, David Cameron
Image caption Praministan Birtabiya, David Cameron

Gwamnatin Sri Lanka ta gaggauta fitowa ta yi watsi da kiran da praministan Birtaniya David Cameron ya yi na a gudanar da wani bincike na kasashen duniya, game da zargin aikata laifukkan yaki a kasar.

Mr Cameron ya ce ya yarda za a dauki lokaci mai tsawo kafin a ce an sasanta, amma idan gwamnatin ba ta gudanar da nata binciken ba, game da zargin aikata laifukkan yaki nan zuwa watan Maris, zai bukaci kasashen duniya su

gudanar da bincike game da batun, ta hanyar aiki da hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya.

Praministan ya bayyana haka ne a Sri Lankar, inda ya je domin halartar taron kolin shugabannin kasashen kungiyar Kwamanwelz.

Basil Rajapaksa, ministan raya tattalin arziki, kuma dan uwa ga shugaban kasar, ya shaidawa manema labaru cewa babu shakka kasar ba zata lamunci haka ba.