Za'a sake zabe a wasu sassan Anambra

Zabe a Nijeriya
Image caption Za a yi zagaye na biyu na zaben gwamna a Anambra

Hukumar zabe ta kasa a Nigeria ta ce za ta sake gudanar da zaben gwamna a wasu sassa na jihar Anambra saboda matsalolin da aka fuskanta wurin gudanar da zaben.

Hukumar dai ta ce kawo yanzu jami'yyar APGA mai mulkin jihar ce kan gaba da kuri'u 174,710, jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria na biye da kuri'u 94,956 yayinda babbar jam'iyyar adawa ta APC ke da kuri'u 92,300.

Sai dai hukumar ta ce ba za ta iya baiyana wanda ya yi nasara ba sai bayan kammala ragowar zaben saboda kuri'un da suka rage ba'a kada ba sun dara tazarar da ke tsakanin jam'iyyar da ta zo ta daya da kuma mai bin ta.

Hukumar dai ta bayyana sakamakon zaben ne a daidai lokacin da 'yan takarar wasu jam'iyyu da suka hada da APC da Labour da PDP suka yi wani taron manema labarai a jiya, inda suka nuna rashin amincewarsu da zaben.

Wasu kungiyoyi masu zaman kansu ma dake sa ido a zaben, sun nuna rashin gamsuwarsu da yadda aka gudanar da shi.

Rahotanni sun ce ba'a kai kayan zabe da wuri ba a wasu mazabu, kuma a rajistar masu zaben ma babu sunayen mutane da dama, kazalika ma suka ce akwai wasu wuraren da ba a yi zaben ba.

Karin bayani