APC ta nemi a soke zaben Anambra

apc
Image caption Bisi Akande na jam'iyyar APC

Jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria ta bukaci hukumar zabe ta kasar, ta soke zaben gwamnan jihar Anambra wanda aka gudanar ranar Asabar da kuma wanda aka karasa ranar Lahadi.

Jam'iyyar ta yi zargin cewa kundin rajistar da aka yi amfani da shi a zaben gurbatacce ne.

Ta kuma ce a sakamakon haka an hana dubban magoya bayanta kada kuria'a .

Jam'iyyar ta APC ta kuma ce ta na da kwakkwarar shaida a kan lamarin.

Sai dai hukumar zabe mai zaman kanta ta musanta wannan zargi.

Ta kuma ce ba ta da dalilin soke zaben saboda sahihancin kundin rajistar da aka yi amfani da shi.