Djokovic ya doke Tomas Berdych

Image caption Djokovic ya sami nasara zuwa wasan karshe

Gogaggen dan wasan kwallon Tennis din nan dan kasar Serbia Novak Djokovic ya doke Tomas Berdych na kasar Jamhuriyyar Czech.

Wannan nasarar ta bawa Novak Djokovic cimma wasan karshe na cofin Davis.

Djokovic ya ce wasan akwai tashin hankali musamman a zagaye na biyu.

Dan wasan na biyu a duniya ya samu nasarar wasanni 24.

Karin bayani