Dan gaban Ingila Sturridge ya murmure

Image caption Sturridge ya shirya buga wasan sada zumunta

Dan gaban Ingila Daniel Sturridge ya murmure kuma zai iya buga wasan sada zumunta da Jamus a Wembley ranar Talata.

Dan wasan mai shekaru 24 dan gaban Liverpool bai buga wasan Ingila da Chile bana ranar Juma'a saboda rauni a sahu da ya ji.

Jamus kuwa za ta rasa dan wasan Arsenal Mesut Ozil da kuma Philipp Lahm da Manuel Neuer duka 'yan Bayern Munich.

A bangaren Ingilar kuma dan bayan nan Phil Jones ba zai buga wasan ba saboda ciwon kwankwaso.

Karin bayani