Kamaru za ta buga gasar kofin Duniya

Image caption Kamaru ta sami galaba kan Tunisia da ci 4-1

Kamaru ta fito gasar cin kofin kwallon kafa na Duniya bayan da ta lallasa Tunusia da ci hudu da daya.

Da farko dai a zagaye na farko Kamaru ta ci Tunisia biyu ba ko daya.

Da aka dawo hutun rabin lokaci Tunusia ta yi azama inda ta rama kwallo daya.

Tunisiyar na ci; kamar an yiwa Kamaru allura ne inda Kamarunta karawa Tunusia kwallo ta uku da ta hudu.

Kamarun dai tabi sahun wasu kasashe a Nahiyar Afrika da suka fito gasar Kamar: Najeriya da Ivory Coast.

Karin bayani