Tripoli ta sallami sojin sa kai na Misrata

Masu zanga-zangar nuna bukatar mayakan sa kai su bar Tripoli
Image caption Masu zanga-zangar nuna bukatar mayakan sa kai su bar Tripoli

An bai wa sojin sa kai na birnin Misrata dake yammacin Libya wa'adin kwanaki uku su fice daga Tripoli babban birnin kasar.

Majalisar karamar hukumar Misratan ce da ta dattawan yankin suka umurce su da su fice su koma yankinsu.

A ranar Jumma'a ne aka yi wata mummunar arangama tsakanin sojin sa kai na Misratan da wasu masu zanga-zangar dake kokarin fatattakar su daga sansanoninsu dake birnin Tripoli inda aka kashe mutane 43 tare da raunata wasu daruruwan mutanen.

Shekaru biyu kenan bayan hambarar da gwamnatin shugaba Mu'ammar Gaddafi tare da kashe shi, to amma har yanzu zababbiyar gwamnatin kasar ba ta da iko da kungiyoyin sojin sa kai na kasar.

Karin bayani