An kama masu safarar mutane a Nijar

Shugaban Nijar, Mahammadou Issoufou
Image caption Shugaban Nijar, Mahammadou Issoufou

Hukumomi a Jamhuriyar Niger sun kama kusan mutane 30 ciki har da jami'an tsaro a kokarin hana safarar mutane, tun bayan da aka gano gawarwakin 'yan cirani fiye da 90 a hamadar sahara, a watan da ya gabata.

Galibin wadanda suka rasun mata ne da kananan yara.

Masu aiko da rahotanni sun ce kamen ya nuna mai yiwuwa wasu hukumomi na taimakawa 'yan ciranin ketara hamadar.

Gwamnatin ta ce ta kudiri aniyar toshe dukkan kafofin damasu fasakwaurin mutanen ke bi.

Tuni gwamnatin ta sanar da shirin rufe dukkan sansanonin 'yan cirani a arewacin kasar.

Karin bayani