Ba bukatar rundunar 'yan sandan jiha - Ribadu

Image caption Nuhu Ribadu: A yi hattara da rundunar 'yan sandan jiha

Dan takarar shugabancin Nigeria a zaben 2011 karkashin rusasshiyar jam'yyar ACN, Malam Nuhu Ribadu ya shawarci gwamnonin kasar da su janye kokarin da suke yi na ganin an amince da kafa rundunonin 'yan sanda na jiha-jiha.

A karshen makon da ya gabata ne, kungiyar gwamnonin kasar bangaren gwamna Rotimi Ameachi suka gudanar da wani taro a Sokoto inda suka bayyana kudurinsu na ci gaba da fadi-tashin ganin sun samu ikon kafa hukumomin 'yan sanda karkashin ikon gwamnonin jihohi.

Gwamnonin dai na zargin gwamnatin tarrayyar kasar wadda ke da iko da rundunar 'yan sanda da amfani da su wajen cin zarafin abokan adawa.

To amma Malam Nuhu Ribadu, wanda tsohon dan sanda ne, yace hakan zai kara matsalar ne saboda babu wani abin da zai hana gwamnoni yin amfani da 'yan sandan kamar yadda su ke zargin shugaban kasa yana yi.

A cewarsa, mafita ita ce a baiwa 'yan sanda cin gashin kansu sannan a ware musu kudin tafiyar da aiki kai tsaye ba tare da ya bi ta hannun gwamnatin tarayya ba.

Karin bayani