Fletcher da Mulgrew ba za su buga wasa ba

Image caption Fletcher bai gama murmurewa ba

Gogaggun 'yan wasan nan Scotland Steven Fletcher da Charlie Mulgrew ba za su buga wasan sada zumunta da Norway ba ranar Talata.

Haka ma dai dan bayan nan na Blackburn Rovers Grant Hanley yana fama da rauni.

Mulgrew ya sami rauni aka bashi izinin ya koma kulob dinsa na Celtic saboda tsare-tsaren wasannin Kulob dinsa na gasar Champions League.

Fletcher kuwa dawowarsa ke nan wasa da Sunderland saboda rauni an kuma hakure masa ya sake samun sauki.

Karin bayani