An gama taron Commonwealth a Sri Lanka

Shugabannin kwamanwelz
Image caption Shugabannin kwamanwelz

Shugabannin kungiyar Commonwealth sun kammala taron kolin da suka gudanar a Colombo babban birnin kasar Sri Lanka.

A sanarwar bayan taro da suka fitar shugabannin sun jaddada kudirinsu na cigaba da muhimman manufofin kungiyar, wandanda suka hada da bunkasa dimokradiyya da kuma kare hakkin bil Adama.

Sun kuma ce shi ma batun sauyin yanayi na ci gaba da zama babbar barazana ga kasashe.

A taron manema labarai shugaban kasar Sri Lankan Mahinda Rajapaksa ya ce kasarsa na bukatar karin lokaci domin dinke barakar da ta biyo bayan yakin basasar kasar.

Taro na gaba na kungiyar za a gudanar da shi ne a kasar Malta, cikin shekaru biyu masu zuwa.