Bafaranshen da aka kama a Nigeria ya isa gida

Francis Collomp
Image caption Francis Collomp ya tsere akan Acaba lokacin da masu tsaronsa suke sallah.

Bafaranshen nan da aka sace a Nigeria ya isa gida bayanda ya tsere daga wadanda suka yi garkuwa da shi a wani yanayi da shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ce yayi kama da littattafan labarai.

Danginsa da Pirai Ministan Faransa ne suka tarye shi a filin saukar jiragen sama.

A watan Disamba ne kimanin 'yan bindiga 30 suka sace Mr Collomp a kauyen Rimi dake jihar Katsina, inda yake aikin samar da wutar lantarki.

A cewar 'yan sandan Nigeria, injiyan ya tsere ne ta hanyar hawa babur din Acaba bayanda fice daga dakin da yake ciki lokacin da masu tsaronsa suke sallah.

Kungiyar Ansaru mai alaka da al-Qaeda ta ce ta kama shi ne don daukar fansa kan tura sojojin Faransa zuwa arewacin Mali.