Tasirin Commonwealth a yau

shugabannin kasashen Commonwealth
Image caption Shugabannin kasashen Commonwealth a Sri Lanka ba su baiyana matsaya game da zargin keta hakkin bil'adama ba.

An gudanar da taron cikin rudani musamman takaddama tsakanin Britaniya da mai masaukin baki, Sri Lanka game da zargin keta hakkin bil'adama lokacin yakin basasar kasar.

Sai dai jawabin bayan taron shugabannin kasashen Commonwealth bai tabo batun ba ko kuma na kin amincewar pirai ministoci uku su ziyarci Sri Lanka.

Maimakon haka, jawabin ya jaddada kudirin shugabannin ne na kare da kuma bunkasa abinda suka kira "manyan manufofin" kungiyar, da suka hada da dimokradiyya, kare hakkin bil'adama da kuma 'yancin fadin albarkacin baki.

A karshen taron kuma, shugaban kasar Sri Lanka, Mahinda Rajapaksa ya kare gwamnatinsa, tare da kafewa cewar kasarsa na neman karin lokaci kafin warware rikicin da ya biyo bayan kammala yakin basasar kasar.

Magen Lami

To, idan har taron bai tattauna wadannan batutuwa masu sarkakiya da kawo rarrabar kai ba, me shugabanin suka tattauna akai?

Kasashe 50 da suka samu wakilci a taron sun mai da kai ne wurin yaki da talauci ta hanyar bunkasa daidaituwa tsakanin kasashen duniya.

Sun kuma amince cewa sauyin yanayi na matukar barazana ga dukkan kasashen duniya.

Hakan ya sa wasu manazarta ke kallon kungiyar a matsayin magen Lami; ba cizo, ba yakushi.

Masu kare kungiyar dai, kamar sakatarenta Kamalesh Sharma sun yi watsi da zargin cewa kungiyar na kau da kai idan ta hadu da matsala ko kuma ta boye zargin keta hakkin bil'adama.

Sai dai kuma masu suka na cewa don me kungiyar ta kasa fid da matsaya game da rashin halartar pirai ministocin Canada, India da Mauritius saboda zargin keta hakkin bil'adama da Sri Lanka ta yi?

Dalili ke nan da har yanzu wasu ke ganin taron na Sri Lanka ya kasa bada amsa kan tambayar da ake yawan yi, wai shin mecece tasirin Commonwealth a wannan zamani?