Jirgin kasa ya kashe mutane 26 a Egypt

Jirgin kasa ya talitse motar hayis da mutanen cikinta
Image caption Jirgin kasa ya talitse motar hayis da mutanen cikinta

Akalla mutane 26 ne suka rasu yayinda wasu 28 suka jikkata a wani hatsarin jirgin kasa da motar hayis da kuma a-kori-kura a Cairo, babban birnin Egypt.

'Yan sanda sun ce mafi yawan wadanda hatsarin ya rutsa da su dangi daya da suke dawowa daga gidan biki a cikin hayis.

Jiragen kasan gwamnatin Egypt dai na yawan samun hatsari.

A watan Janairu, mutane 19 ne suka rasu lokacinda wani jirgin kasa da ke dauke da kuratan soja ya sauka daga hanyarsa, a bara kuma kusan yara 50 ne suka rasu lokacin da jirgin kasa ya yi karo da motar da ke kai su makaranta bayanda mai ba jirgin hannu ya yi bacci.