Ana neman wani dan bindiga a Faransa

'Yan sanda a Faransa
Image caption 'Yan sanda a Faransa

'Yan sanda a Faransa na neman wani dan bindiga da ya bude wuta a hedkwatar jaridar Liberation dake birnin Paris da kuma bankin Societe Generale.

Shugaban sashen gabatar da kara na birnin Paris, Francois Molins, ya ce wani hoton bidiyo da ma albarushin da aka yi amfani da shi sun nuna cewa, mutumin da ya kai hare-haren, shi ne ya yi barazana ga wasu 'yan jarida a wani gidan talabijin ranar Juma'a.

Mista Molins ya ce, mutumin da ake nema wani mai kama da mutanen Turai ne, sanye da safar hannu da korayen takalma.

Dan bindigar ya tsere ne ta hanyar tare wata mota, wadda ya tilasta wa direbanta ya kai shi babban titin nan na Champs-Elysees mai cike da jama'a.

Wani mai daukar hoto ya yi rauni a gidan jaridar ta Liberation.