Sturridge zai buga wasan Jamus

Image caption Sturridge ana shakku ko zai iya buga wasa da Jamus

Kochiyan Ingila Roy Hodgson ya ce Daniel Sturridge zai buga wasan Jamus ya kara da cewa ya fitar da shi ne a motsa jiki ranar Litinin da safe don ya murmure.

Ya yi motsa jiki na mintina 45 ranar Litinin kafin ya bar filin wasan tare da Likitan Ingila Steve Kemp.

Dan wasan mai shekaru 24, dan gaban Liverpool bai buga wasan Ingila da Chile ba ranar Juma'a saboda rauni a sahunsa.

Daniel Sturridge ya ce ya murmure zai iya buga wasan na Jamus.

Jamus dai ita ma ta fito gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za ayi a Brazil 2014.

Karin bayani