Za'a tsaurara matakan kare yara a intanet

Image caption Yada hotunan batsa na kananan yara a intanet na karuwa

Manyan kamfanonin matambayi-baya-bata na intanet, Google da Microsoft sun amince da matakan hana yada hotunan batsa na kananan yara a intanet.

Kamfanonin sun ware fiye da kalmomi dubu 100 wadanda duk wanda ya yi amfani da su wurin bincike zai samu sakon gargadi cewa yada hotunan batsa na kananan yara haramun ne.

Pirai ministan Britaniya David Cameron, wanda ya bukaci kamfanonin su dau wannan mataki ya yi maraba da batun, sai dai ya ce idan bai gani a aikace ba zai gabatar da dokar da zata hukunta su.

Shafukan matambayi-baya-bata na Google da Bing mallakar Microsoft su ke gudanar da kaso 95 na binciken da ake yi a intanet.

Ba'a nan take ba

Kwararru kan kare hakkin yara na cewa yawancin masu yada hotunan batsa na kananan yara a intanet ba sa amfani da shafukan matambayi-baya-bata.

Kan haka ne, kamfanonin Google da Microsoft suka amince su hada kai da hukumar yaki da manyan laifuffuka ta UK da Gidauniyar sa ido kan intanet domin tona asirin maboyar da masu laifin ke amfani da su.

Kamfanonin biyu kuma na amfani da fasaha wurin gano asalin inda duk wani hoto ya fito da kuma duk wani shige da fice da zai yi a shafukan intanet.

Sai dai manazarta na ganin gwamnatin Britaniya na yin kasa a gwiwa wurin yaki da masu lalata da yara ta hanyar intanet din.

Sakamakon haka suke bukatar gwamnatin ta karawa hukumar yaki da manyan laifukan kudin da take bata a kasafin kasa saboda ta inganta aikinta.