India: Abin da ya sa 'yan Nigeria ke tserewa daga Goa

Image caption Goa ta yi fice wajen yawon bude ido

'Yan Najeriya na ci gaba da ficewa daga jihar Goa saboda musgunawar da suka ce ana yi musu tun daga ranar 31 ga watan Oktoba lokacin da suka yi zanga-zanga domin nuna rashin jin dadinsu da kisan da aka yi wa dan uwansu.

Akasarin 'yan Nigeria da ke jihar sun fice daga cikinta inda suka koma jihohin da ke yammacin kasar kamarsu Pune da Mumbai.

A jihar Goa, 'yan sanda na yin bincike sosai domin korar bakaken fata 'yan asalin Africa daga jihar.

Jihar Goa ta yi fice wajen wuraren shakatawa da tekuna da wuraren holewa, lamarin da ke jan hankalin masu yawon bude idanu daga Rasha da wasu kasashen Turai, da ma 'yan India da ke zuwa hutu.

Ya kamata a yi taka-tsantsan

'Yan Africa sun fi zama a kauyukan Parra da Siolim da ke jihar Goa - kusa da wuraren shakatawa da ke bakin tekunan Baga da Calangute da kuma Anjuna.

Sai dai a yanzu, dagatan kauyukan sun yanke shawarar hana a bai wa 'yan Nigeria hayar gidaje.

Kazalika wata kungiyar masu ababen hawa ta daina daukar 'yan Nigeria saboda nuna rashin jin dadi da matakin da 'yan Africa guda 60 -- yawancinsu 'yan Nigeria -- suka dauka a watan jiya na datse hanya saboda zargin cewa ana musguna musu.

Akwai 'yan Nigeria kimanin 40,000 a India, kuma da dama daga cikinsu suna zaune ne a jihar Goa.

Jakadan Nigeria a India, Ndubuisi Vitus Amaku, ya shaidawa BBC cewa 'yan Nigeria na cike da bakin ciki bayan kashe dan uwansu Mista Simeon, da kuma umarnin da mahukuntan jihar suka bayar na fitar da 'yan Nigeria daga cikinta.

Ya gargadi mahukuntan India su yi taka-tsantsan kan matakin da suke dauka, yana mai cewa idan suna da matsala da 'yan Nigeria ya kamata su dauki matakin shari'a maimakon musguna musu.

Karin bayani