An kashe mutane bakwai a Filato

Image caption Tarok sun zargi Fulani, amma Fualnin sun musanta

Rahotanni daga jihar Filato a Nijeriya na cewa mutane akalla bakwai ne suka rasa rayukansu, wasu kuma suka samu raunuka, a sakamakon wani farmaki da wasu 'yan bindiga suka kai a wani kauye a karamar hukumar Shendam.

'Yan kabilar Taroh dai na zargin Fulani makiyaya da kai masu harin.

Sai dai Fulanin sun musanta hakan.

Jihar dai na fama rikice-rikicen da suke da nasaba da addini da kabilanci da siyasa.

Karin bayani