Takun saka tsakanin Indonesia da Australia

Image caption Wannan dai shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin zarge-zargen leken asiri da suka sa dangantaka tsakanin kasashen biyu kawayen juna ta yi tsami.

Shugaban kasar Indonesia ya bukaci Australia ta yi bayani cikin sauri, kan zargin cewa hukumar leken asarin kasar ta saci hirar wayarsa, a wani abu da ya kara zurfafa rashin jituwa tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Susiloo Bambang Yudho-yono ya zargi Firayin Ministan Australiar Tony Abbott da nuna ko-oho game da batun wanda ya ce ya kona masa rai ainun.

A yanzu dai Indonesia ta mai do da jakadanta da ke kasar Australia gida ranar litinin bayan wannan zargin ya bayyana, kuma ta ce za ta kira jakadan Australiyar da ke kasar domin yi masa tambayoyi.

Da yake mai da martani kan zargin gaban majalisar dokokin kasarsa, Mr. Abbot yace ya yi matukar nadamar duk wani cin fuska da aka yiwa shugaban na Indonesia.

Sai dai ya ce gwamnatin Australiya ba za ta ce komi ba kan wani abu da ya shafi tattara bayanan sirri , saboda kowace gwamnati na tattara bayanan sirrin kuma kowace gwamnati ta san duk gwamnati na yin hakan.

Karin bayani