Jonathan zai gabatar da kasafin kudi a yau

Image caption 'yan majalisar kasar dai na ganin gwamnatin bata aiwatar da ko kashi 40% na kasafin kudin wannan shekara ba.

A yau Talata ne Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan zai gabatar da kudurin kasafin kudin kasar na badi.

Tun da farko dai shugaban kasar ya shirya gabatar da kasafin kudin ne a ranar talatar da ta gabata, amma daga bisani ya aikewa 'yan Majalisun da wata wasika in da ya shaida musu cewa ba zai samu damar gabatar da kasafin kudin ba sai a wannan lokacin.

Shugaban kasar dai bai bayyana dalilin dage gabatar da kasafin ba.

Mista Jonathan dai zai gabatar da kasafin kudin ne a daidai lokacin da 'yan majalisun dokokin kasar ke kukan cewa bangaren zartarwa bai tabuka wani abin kirki wajen aiwatar da kasafin kudin shekara mai karewa ba, musamman wajen aiwatar da manyan ayyuka.

Karin bayani