Najeriya ta tura 'yan sanda aiki waje

'Yan sandan Najeriya
Image caption Najeriya ta ce inda aka tura jami'an nata sun fi kasar bukatar aikin 'yan sandan

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta sake tura tawagar 'yan sanda da ta kunshi jami'ai 400 aikin tabbatar da zaman lafiya.

'yan sandan za su yi aiki ne da rundunar Majalisar Dinkin Duniya da ke Liberia da kuma Darfur a Sudan.

Hukumomi sun ce hakan na daga taimakon da Najeriya ke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Afrika da kuma duniya.

A yanzu haka akwai tawagar 'yan sandan Najeriya da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a kasashen Afrika tara.

Karin bayani