An kashe mutane 10 a Somalia

Image caption Mayakan Al- Shabaab

Akalla mutane goma ne aka bada rahoton sun rasu a Somalia a wani harin kunar bakin wake da aka kai wani ofishin 'yan sanda a garin Beledweyne.

Wakilin BBC a Somalia ya ce ana amfani da chaji ofis din 'yan sandan ne a matsayin sansanin sojojin Djibouti dana Ethiopia wadanda ke aiki karkashin rundunar kiyaye zaman lafiya na Afirka watau AMISOM.

Kungiyar gwagwarmaya ta Al Shabaab ta yi ikrarin cewa ita ce ta kai harin.

A watan da ya gabata ma kungiyar Al Shabaab ta ce ita ce ta kai wani hari a garin, lamarin da ya janyo mutuwar mutane 16.