Za a tantance yawan 'yan Somalia a sansanin Dadaab

Image caption Kenya dai ta shiga kokarin ganin ta rabu da 'yan somalian ne tun bayan harin da mayakan Alshabaab suka kai kan kasuwar West Gate a watan jiya.

Majalisar Dinkin Duniya na shirin yin wani bincike a daya daga cikin sansanonin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya da ke Dadaab a arewacin kasar Kenya; domin sanin ko mutun nawa ne daga cikin 'yan asalin kasar Somalia su kusan 500,000 ke zaune a wajen ke son komawa kasarsu.

A makon jiya ne Kenya da Somalia suka rattaba hannu a kan wata yarjejeniya da Majalisar Dinkin Duniya ta soma wani shiri na mai da 'yan Somalian kasarsu.

Sai dai masu aiko da rahotanni sun ce kadan ne daga cikin 'yan gudun hijirar suka nuna sha'awar komawa Somalia.

Daya daga cikin 'yan gudun hijirar ya shaidawa BBC cewa har yanzu Somalia na da matukar hadari saboda karfin da kungiyar Al-shabaab ta ke da shi a can.

''Babu cikakken tsaro a Somalia, don haka bamu da niyyar komawa wannan kasar baki daya, idan muka koma 'ya'yan mu ba za su samu ilimi ba,karshe ma tashin hankali za a cigaba da yi, in ji