Sojojin Congo zasu fuskanci kuliya

Image caption Dakarun Congo a garin Goma

Za a fara shari'ar sojojin Congo 39 wadanda ake zargi da aikata fyade a garin Goma dake gabashin Jamhuriyar dimokradiyar Congo.

Masu binciken kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya, sun ce mata fiye da 100 ne da kuma yara 'yan mata 30 suka gamu da cin zarafinsu ta hanyar lalata daga sojojin gwamnatin Congon a watan Nuwambar bara.

Wani wakilin BBC a Goma ya ce shari'ar sojojin ta biyo bayan matsin lambar da kasashen duniya suka yi ta yi tsawon watanni.

Da farko rundunar sojin Congon ta dakatar da sojoji 23 ne, amma babu wanda aka gabatar gaban shari'a har sai da Majalisar Dinkin Duniya ta yi barazanar dakatar da tallafin kudi ga bangarorin sojin da ake zargi da fyaden.

Karin bayani