An gabatar da kasafin kudin 2014 a Ghana

Shugaba John Dramani Mahama na Ghana
Image caption An gabatar da kasafin kudin yayin da 'yan kasar ke kokawa da tsadar rayuwa

Ministan kudin Ghana Seth Tekper ya gabatar da kasafin kudin kasar na badi a gaban majalisan dokokin kasar.

A ranar Talata ne , ministan kudin wanda ya shafe kusan sa'o'i uku yana gabatar da kasafin kudin ya ce kasafin kudin zai haifar da gibin sama da sabon cedi miliyan dubu takwas.

Mr Tekper ya ce yawan kudaden da gwamnatin take sa ran samu ta bangaren haraji da sauransu bai fi sabon cedi miliyan dubu 25 da 'yan kai ba a yayin da take sa ran kashe sama da sabon cedi miliyon dubu talatin da hudu a wajen ayyukan gina kasa.

Hakan na zuwa ne a dai dai lokacin da 'yan Ghana, ke korafi a kan tsadar rayuwa a kasar.

Karin bayani