An damke Fasto kan sayar da jaririya a Imo

Image caption Speto Janar na 'yan sandan Nigeria, Muhammed Abubakar

Rundunar 'yan sandan jihar Imo a kudancin Nigeria ta damke mutane uku, bisa zargin sayar da wata jaririya wadda 'yar faston ta haifa bayan ta yi cikin shege.

Mutanen da rundunar 'yan sandan ta jihar Imo ta kama, sun hada da Fasto Michael Ogugua na cocin Eleventh Hour Deliverence Ministry da ke garin Ejemekuru na yankin karamar hukumar Oguta na jihar ta Imo, da wani likita mai suna Dokta Cyprian Pat, wanda ke da wani asibiti mai zaman kansa, Newlife Clinic da ke birnin Fatakwal na jihar Ribas, da kuma wata dalibar jami'ar jihar Abia.

Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar 'yan sandan jihar Imo, DSP Joy Elemoko ta tabbatar da BBC afkuwar lamarin inda tace suna ci gaba da bincike.

An kuma kame su ne, ta hanyar wasu bayanai da aka tsegunta wa 'yan sanda, bisa zargin cuwa-cuwar sayar da wata jaririya, wadda 'yar faston ta haifa, a kan kudi naira dubu dari biyu.

Yayin da 'yar faston ke kukan a kawo mata 'yarta, har yanzu ba a san yadda aka yi da jaririyar ba.

Batun safarar jarirai dai na ci gaba da zama wata babbar matsala tare da daukar sabon salo a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya.

Wata yarinya ce 'yar shekara goma sha bakwai ta yi ciki, amma sai mahaifinta wani Rabaran Ogugua ya ce ta je ta zubar da cikin. Ko da ta ki bin umarnin nasa na neman zubar da cikin, sai yak ore ta daga gidanasa.

Karin bayani