Tattaunawa ta yi dadi, amma ba yarjejeniya kan nukiliyar Iran

Taro kan nukiliyar Iran
Image caption Taro kan nukiliyar Iran a Geneva

Amurka ta bayyana tattaunawar baya bayan nan a kan shirin Nukiliyar Iran a matsayin mai fa'ida, to amma ta ce ba ta saurin ganin kulla wata yarjejeniya.

Wani babban jami'in Amurka ya ce zai yi wuya a cimma yarjejeniya a lokacin tattaunawar wadda aka kome tsakanin Iran da manyan kasashen duniya a Geneva.

Ana sa ran ci gaba da shawarwari a gobe alhamis.

Tun fako jagoran addini na kasar ta Iran Ayatollah Ali Khamenei ya ce gwamnatin Iran ba za ta saki yancinta na mallakar wani shirin nukiliya ba.

Manyan kasashen duniyar dai na fatan cimma wata yarjejeniyar wucin gadi da zata sa Iran ta daina shirinta na Nukiliya domin samun sauki daga takunkumin kasashen duniya.

Tun farko kuma Shugaba Barack Obama ya bukaci 'yan majalisar dattawan Amurka da ka da su sanya wa Iran sabbin takunkumi.

Su bari a ga yadda tattaunawar diflomasiyyar da ake yi za ta kaya.

Karin bayani